
Kotun sauraran kararrakin zabe a Kano ta kori karar da Umar Abdullahi Ganduje ya shigar yana kalubalantar zaben da aka yiwa Tijjani Abdulkadir Jobe a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado.
Abba dai ya shigar da karar ne yana kalubalantar nasarar da Tijjani Abdulkadir Jobe na jam’iyyar NNPP ya samu a zaben kujerar dan majalisa a mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado daga Jihar Kano.
Alkalan kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a I.P Chima ne dai suka yi fatali da karar ranar Talata saboda rashin kwararan hujjoji daga bangaren masu kara.
Haka kuma kotun ta ce masu shigar da karar sun gaza gabatar da kwararan hujjojin da za su gasgata zarge-zargen da suka yi a yayin zaben.
Kazalika, kotun ta umarci Abba Ganduje ya biya Jobe Naira dubu 200, saboda bata masa lokaci.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai ta ayyana Jobe a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.
Umar Abdullahi Ganduje shine dan tsohon Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ake yiwa lakabi da Abba Ganduje ya garzaya gaban kotu yana neman ta soke nasarar Joben..