Mazauna unguwar Doka, Baici a karamar hukumar Tofa ta Kano, sun shiga cikin kaduwa da alhini, sakamakon rasuwar wata jaririya da ake zargin mahaifinta ya sa mata guba.
Wanda ake zargin, Misbahu Salisu mai shekaru 28, an kama shi ne watanni 3 bayan aikata laifin.
A bayaninsa jim kadan bayan da jami’an Hisbah suka yi nasarar kama shi, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya sanya fiya-fiya a shayin da ya bai wa jaririyar wacce kwananta daya da haihuwa, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.
Ya ce kafin hakan, sai da ya sanya wa mahaifiyar jaririyar wato Matarsa mai suna Sa’ade kwaya a shayinta, wanda ya sa ta fita hayyacinta, kafin ya aikata ta’asar.
Misbahu ya amsa laifinsa, inda ya ce, ya fi son da namiji, amma matarsa ta haifa masa mace, wanda hakan ya sa shi kashe ta.
A jawabinsa, mataimakin kwamanda janar mai kula da ayyuka na Hukumar Hisbah, Dr. Mujahid Aminudeen, ya ce Misbahu ya amsa laifinsa, kuma za a mika shi ga hukumar binciken manyan laifuka ta kasa (CID), domin daukar matakin da ya dace.
Ya kara da cewa, hukumar Hisbah ta jihar Kano, ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na tsaftace Kano, ba tare da wata muguwar dabi’a ba, domin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, mataimakin kwamanda janar din ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wanda ake zargi ga hukumomin da abin ya shafa, domin dakile laifuka a jihar.
Daga Khadijah Aliyu