Masu jajayen huluna ne suka kore mu daga Kano – Alƙalan Kotun Zaɓe

0
274

Alkalan da suka yi shari’ar zaben Kano sun yi raddi dangane da kalaman da wasu ‘yan jam’iyyar NNPP a jihar suka yi gabannin yanke hukuncin da ya bai wa Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC Nasara.

Hukuncin da alkalan suka karanto a shari’ar da aka gudanar a ranar Laraba ta manhajar Zoom inda daya daga cikin alkalan da suka yanke hukunci Mai Shari’a Benson Anya ya caccaki ‘yan Kwankwasiyya.

A yayin da yake karanto hukuncin shari’ar zaben, ya ce bai kamata saboda jita-jita na yawo kan cewa ba za su yi nasara a kotu su rinka barazana ga alkalai ba.

“Kuskure ne a razana siyasar Kano baki dayanta da tarzoma. Kada jam’iyya ta kuskura ta yi wa jama’a barazana da ta’addanci da tashin hankali. Kada a dauki hukuncin kotu da zafi wanda har zai sa a kai hari kan ma’aikatan kotu, kamar yadda wakilan wadanda ake kara na biyu da na uku suka yi.,” in ji Mai Shari’a Anya.

“Ina amfani da wannan damar domin yin tir da gungun masu jajayen huluna wadanda ke kama da ‘yan ta’adda, inda suka kore mu daga Kano tare da saka rayukanmu cikin fargaba. Mun yi amannar cewa Allah kadai ke ba da mulki.

“Dole wadanda suka yarda da Allah su amince da hakan da kuma mubaya’a ga karfin gwamnati,” in ji shi.

Ya bayyana cewa daukar doka a hannu da tayar da tarzoma ba zai taba zama wata hanya ta samun karfin iko ba.

“Yi wa rayukan alkalai barazana kamar yadda wasu fusatattun barayi wadanda suke kiran kansu ‘yan siyasa suka yi abin takaici ne,” in ji shi.

A makon da ya gabata ne alkalan kotun sauraran kararrakin zaben karkashin jagorancin Mai Shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay da Mai Shari’a Istifanus Gandu da kuma Mai Shari’a Benson Anya suka ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Kano.

Kwanaki kadan kafin yanke wannan hukuncin, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sallami kwamishinansa Adamu Kibiya sakamakon barazana ga alkalan da ke sauraron shari’ar gwamnan jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here