Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce bai gamsu da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke na korar shi daga kan kujerarsa ba, kuma zai garzaya Kotun Koli.
A ranar Juma’a ce dai kotun ta tabbatar wanda kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na soke nasarar Abban na jam’iyyar NNPP, sannan ta ayyana dan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar.
To sai dai da yake mayar da martani a wani faifan bidiyo da maraicen Juma’a, Gwamna Abba ya ce ba a yi musu adalci ba a hukuncin, amma za su ɗaukaka kara.
A cewarsa, “Wannan kotun, kamar ta baya ma ba ta yi mana adalci ba. Mutanen Kano sun zabe mu, amma wadannan kotunan sun ce wadancan mutanen ne suka ci.
“Tuni mun umarci lauyoyinmu da su da su shigar da wata sabuwar kara a Kotun Koli ta Najeriya. Muna kyautata zaton wannan kotun za ta yi wa al’ummar Jihar Kano ta hanyar dawo musu da abin da suka kwata,” in ji Abba.
Gwamnan ya kuma ba al’ummar Jihar tabbacin cewa za su hada kai da jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu.