Kotun Najeriya ta haramtawa tsohuwar ministar Buhari riƙe kowanne irin muƙami

0
346

Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja ta haramta wa tsohuwar Ministar Mata da Walwalar Al’umma ta kasar, Pauline Tallen sake rike wani mukamin gwamnati a kasar.

A wani hukunci da ta yanke a wannan Litinin, kotun ta yi tur da kalaman da tsohuwar ministar ta yi a bara, inda ta caccaki wani hukuncin kotun tarayya da ke jihar Adamawa.

Kotun da ke zamanta a birnin Yola, babban birnin Adamawa, ta soke cancantar takarar A’ishatu Dahiru da aka fi sani da Binani ta jam’iyyar APC da ke neman kujerar gwamnan a wancan lokacin.

Sai dai Tallen ta nuna rashin gamsuwarta da hukuncin na kotun wanda ta bayyana a matsayin “musguna wa wani bangare na al’umma”, yayin da ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da hukuncin.

Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa, Yakubu Maikyau yaa bukaci Tallen da ta nemi afuwa kan kalamanta, inda har ya yi barazanar maka ta a gaban kuliya.

Sai dai tsohuwar ministar ba ta nuna halin ko-in-kula ba, abin da ya sa kungiyar lauyoyin ta maka ta a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here