Attajiri A.A Rano Zai Jagoranci Tallafawa Ɗaliban Jami’ar Bayero Da Su Ka Gaza Biyan Kuɗin Makaranta

0
626

Shugaban rukunin kamfanin A.A. Rano Alhaji Auwalu Abdullahi Rano ya dau alkawarin tattaro kan Masu Hannu Da shuni domin Tallafawa Dalibai Marasa Karfi na Jami’ar Bayero da ke Kano da kuɗin Makaranta.

Sanarwar ta fito ne ta wata takarda da Daraktan hulda da jama’a na jamiar ta BUK, Malam Garba Lamara ya fitar a jiya Alhamis.

Tun da farko dai hukumar Jami’ar ta Bayero ce ta buƙaci masu hannu da shuni da ke jihar Kano, da su taimakawa ɗalibai marasa karfi musamman ƴan asalin jihar Kano da kuɗin makaranta domin gudun taɓarɓarewar karatun su.

Hamshaƙin Attajirin ya baiwa hukumar jami’ar tabbacin zai haɗo kan masu kudi da kamfanoni da kuma duk masu ruwa da tsaki wajen ganin an haɗa gagarumar gidauniya domin tallafawa waɗannan ɗalibai marasa ƙarfi da su ke karatu a jami’ar ta BUK.

A.A Rani ya yi wannan furucin ne a lokacin da shugaban jami’ar ta BUK Farfesa Sagir Adamu Abbas da tawagar sa su ka kai masa ziyara a ofishinsa. Inda shugaban jami’ar ya bayyana cewa sun ɗauki aniyar nemowa ɗaliban tallafi ne a wurin mawadata saboda halin matsin tattalin arzikin da al’umma suka shiga.

Jami’ar ta Bayero dai ta ƙara wa’adin biyan kuɗin makarantar da kwana Talatin, inda a yanzu za a rufe a ranar 10 ga watan Satumba na wannan shekarar ta 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here