Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da kashe dakarunta 36 a Jihar Neja

0
431

Rundunar tsaron Nijeriya ta tabbatar da cewa an kashe jami’anta 36 a Jihar Neja da ke yankin arewa ta tsakiyar kasar.

Rahotannin farko da suka bayar da labarin sun ce tun a ranar Lahadi da marece lamarin ya faru, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

AFP ya ce ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaron Nijeriyar a kalla 26 sannan suka jikkata takwas a wani harin kwanton-baunar da suka kai musu a tsakiyar kasar.

Sai dai a tasu sanarwar ta ranar Alhamis, rundunar sojin ta bakin daraktan yada labaranta Manjo Janar Edward Buba yayin da yake bayar da bayanai kan yawan wadanda aka kashe din, ya ce dakaru 36 rundunar ta rasa.

Kazalika ya yi bayani kan hatsarin da wani helikwaftan rundunar ya yi ranar 14 ga watan Agustan 2023, a taron na mako-mako kan ayyukan rtundunar da ake bayarwa.

Kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito cewa da aka tambaye shi karin bayani kan hatsarin helikwaftan, sai Manjo Janar Buba ya ce ana ci gaba da bincike don gano abin da ya jawo tare da jan hankalin ‘yan kasa da su guji yarda da farfagandar da ‘yan ta’adda ke yadawa tare da zama masu kishin kasa.

Masu tayar da kayar baya ne suka yi wa dakarun kwanton bauna a yankin Zungeru inda dakarun suka hadu da ajalinsu.

Sannan wani jirgin yaki na rundunar sojin saman Nijeriya ya yi hatsari a ranar Litinin a yayin da yake aikin kwashe wadanda suka mutu a kwanton bauna, a yankin karamar hukumar Shiroro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here