Kotun sauraron ƙorafin zaɓe da ke zama a Kano ta kori ƙarar da Muhammad Ali Wudil na jam’iyyar APC ya shigar gabanta yana ƙalubalantar nasarar Abdulhakeem Kamilu Ado na jami’iyyar NNPP.
Kano Times ta rawaito cewa kutun ta kori ƙarar ne saboda rashin gabatar da gamsassun hujjoji da zasu ƙalubalanci sahihancin tsayawar ɗan takarar zaɓen, majalisar tarayya a ƙananan hukumomin Wudil da Garko, wanda ya baiwa Abdulhakeem Kamilu Ado, na NNPP nasara.
Kotun Mai alkalai Uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ngozi Flora ta bayyana cewa doka ta bawa jam’iyya dama canza ɗan takara bayan mutuwar wani koda babu sunansa a jikin takardun da aka shigarwa INEC matuƙar jam’iyya tabi ta hanyar da doka ta tanada.
Ta Kuma ce mai shigar da karar ya kasa baiwa Kotun hujjojin cewa ɗan takarar bai da katin shaidar zama halastaccen ɗan jam’iyyar na NNPP.
“Saboda haka mun kori wannan karar saboda rashin gamsassun hujjoji” a cewar Mai Sharia Ngozi.
Haka zalika kotun ta umarci wanda ya shigar da ƙarar da ya biya ɗan majalisar tare sa INEC 800,000 saboda ɓata musu lokaci da su ka yi.