Ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar adawar Najeriya, Abubakar Atiku, ya ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙoli, inda ya nemi ta soke hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa, da ya tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2023.
A wata takardar ɗaukaka ƙara da ɗan takarar na PDP ya gabatar bisa wasu dalilai 35. Atiku Abubakar ya ƙara da cewa kotun ta yi manyan kura-kurai da rashin adalci a binciken da ta gudanar.
Ya kuma yi iƙirarin cewa hukuncin da kotun ta yanke, bai yi daidai da ainihin ƙarar da ya shigar ba.
Atiku ya kara da cewa ya kamata kotun ta soke zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, saboda rashin bin dokar zaɓe ta 2022.
Leave a Reply