Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun ba da sanarwar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Talata 3 ga watan Oktoba a fadin kasar.
Kungiyoyin NLC da TUC sun bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka kira da yammacin ranar Talata a babban birnin kasar, Abuja.
Sun bukaci rassansu na jihohi su harhado kan ‘yan kwadago da sauran jama’a don gudanar da jerin zanga-zanga da maci a fadin Najeriya.
Kafofin labarai a Najeriya na cewa sun fahimci cewa shugabannin kungiyoyin kwadagon biyu sun warware bambance-bambancen da suka sanya kungiyar NLC shiga wani yajin aikin gargadi tsawon kwana biyu, ba tare da takwararsu ta TUC ba.
NLC ta kaurace wa aiki a ranakun 5 da kuma 6 ga watan Satumba da muke ciki don matsa lamba ga gwamnatin kasar a kan ta shawo kan wahalhalun da ‘yan Najeriya, musamman ma’aikata ke ciki, sakamakon cire tallafin man fetur.
BBC Hausa
Leave a Reply