Duniya Makwantar Rikici: Dalilin Sabon Rikicin Ƙasar Isra’ila

0
503

Asalin abin da ya haifar da yakin da ake yi a WEST BANK na GAZA shi ne; Ranar Alhamis da ta wuce da daddare sojojin Israila suka shiga yankin Huwwara da zimmar zargin wai wani matashi Musulmi Bapalasdine ya jefe su da hoge. Al’adar sojojin ita ce da zarar, , an samu sabani sai su rika bi gida-gida suna bincike. Akwai tsananin kiyayyar juna da zaman ba a ga maciji. Duk wanda suka tambara, suka nuna shi, sai dai wani ba shi ba, kawai nan take sai su harbe shi Bapalasdine lahira. Palasdinawa sun riga sun saba, wannan ya sanya sun dake har sun zama jan wuya, don haka ba sa daukar raini duk karfin bindigar Yahudun ba sa shayinta. Irin wannan ce ta faru ranar Alhamis.

Amma kamar lamarin jiya Alhamis ya lafa, wayewar gari ranar Juma’a, sai sojan Israila suka sake harbe wani matashin dan shekara 19 mai suna Labeel Muhammad Dumaidi a wani sumemen asubahi da ‘yan kama-wuri zauna suka yi a GAZA. Yaron sun harbe shi ne a kirji suka farfasa masa zuciyarsa. Nan da nan tarzoma ta barke.

A shigowar wannan shekara ta 2023, an samu tashin hankali da tarzoma a tsakanin Palasdinawa a GAZA da sojan mamaya na Yahudun Israeli akalla kamar sau 11. Gaskiya ma dai an samu kusan shekara takwas rabon da a samu rigima a kai, a kai a GAZA kamar ta bana.

Akalla daga Fabrairu 2023, sojan Israila sun hallaka Musulmin Palasdinawa 197. A Gaza kawai an kashe mutum 37. Su kuma Yahudun sun rasa mutum 30. Wannan tsohon rikici ne. Tun shekara 75 da suka gabata ake tashin hankali da yaki a kasar Palasdinu. Yahudawa sun hana Musulmin Palasdinawa wurin zamansu na gado.

Shekara kusan hudu, dama HAMAS suna laluben damar da zasu samu don su gwada kwanjinsu kuma su tunkari Israila, suna burin su samu mukafa’a ta tsaro da intelligence irin na Israila ta yadda, idan aka yi musu kan kara zasu yi na ita ce, in duniya ta ga dama ta shiga tsakani, musamman kuma bayan nasarar zaben Benjamin Netanyahu a matsayin Firaministan Israila.

Haka kuwa aka yi ranar Asabat da asuba, ba zato ba tsammanin HAMAS suka kaddamar da yaki akan Israila. Tun shekarar 1973 kasar Israila bata taba samun tashin hankali ba kamar na shekaran jiya. A labarai na kafafen Turai a ranar Asabat kadai da soja da farar hula sama da 700 na Israel suka hallaka, kuma an yi garkuwa da akalla mutum 150 suna hannun yan HAMAS. Wannan hari ya baiwa duniya mamaki saboda irin tanadin tsaro da karfin bincike na sirri na Israila take da shi, amma Palasdinawa suka karya lagon da suke takama da shi.

Yaki gadan-gadan na kan mai uwa da wabi ya barke, kuma duk wata sa’a a cikin kwana biyun nan, sai an kashe rai, an zub da jini, duk duniya kuma ta dauki dumi.

Bello Muhammad Sharada

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here