Su Rarara kafin a ci arzikin Buhari ayi ɓulɓul

0
230

Na san daga ranar Alhamis 27 ga Oktoba 2023, lokacin da Rarara ya saki bama-bamai a kan tsohon Shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, an yamutsa hazo da ƙalubale da caccaka. Wannan ya sa na laluba cikin duhun rumbun ajiya ta, na zaƙulo wata waƙa da na ji ta gamayyar mawaƙa, wacce shi Rarara ɗin ya jagoranta, don tuni da yadda ya fara. Amshin wakar, wanda kuma ya zamar mata jigo da kuma jagora shi ne:

/Ban ga hujjar da za zagen, tun da ban je gidan ka maula ba /
Ban ga dalilin da za ka zage ni, tun da ba taimako na nema ba /
Ban ga hujjar da za zagen, tun da ban ce ka bani lallai ba /
Mawaƙa bBa Maroƙa ba / Maroƙa / Ba ɓarayi ba

A ɗan binciken da na yi, wannan waƙar ta samo asali daga ƙalubalen da aka dinga yiwa mawaƙa a lokacin wata rigima da ƴan fim a matsayin su maroƙa ne. Wannan ta hassala waɗansu daga cikin mawaƙan, har suka yi gangami, suka yi wannan waƙar, amma Rarara ne jagoran ta. Mawaƙan sun haɗa da Amin Afandaj, Abubakar Sani, Adamu Nagudu, Hussain Danko, Sani Hassan, Auwal Ishaq, Sabon Zuwa Nabori, da kuma Zuwaira M Inuwa.

Waƙar na da ban mamaki saboda yadda ta so ta harɗe kanta – “mawaƙa, ba maroƙa ba”, sannan sai “maroƙa, ba ɓarayi ba”. To in ba rami, mai ya kawo maganar rami? Sannan kuma a cikin baitukan Sani Hassan, akwai inda ya ke cewa:

/In na ga dama in rera waƙa a kanka ba don ka bani komai ba /
Kuma in za ka ban na karɓa, don kuwa Musulmi ba zai ƙi kyauta ba /
Ni ba bara nake ba, kuma ban ce ka bani rance ba /

Kamar sauran CDs na mawaƙan Hausa a wancan lokacin, babu wata rana ko shekara da aka buga a jikin kwalin CD ɗin, amma tabbas kafin farkawa da social media na mawaƙan Hausa ne wajen 2013. Kalli Rarara a jaket din, kafin ya ƙoshi da ƙuɗin ƴan siyasa ya yi ɓulɓul!– har da magoyan Buhari da yanzu ya ce ya yi nadamar tafiyar sa (watakila kuma ya mayar da kuɗaɗen da ya yi a inuwar Buharin).

Gata nan, za ta zo ku ji ta!
https://bit.ly/49epHEI.

Daga Shafin Farfesa Abdullah Uba Adamu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here