Gwamnonin PDP za su tattauna don sulhunta Wike da Gwamna Fubara

0
285

Saɓanin wani sauyi ko canjin al’amari, ana sa ran a yau Talata gwamnonin PDP za su tattauna don ganin sun sulhunta takun saƙar da ke tsakanin Ministan Abuja Mr. Wike da kuma gwamnan jihar Ribas Similanayi Fubara.

Gwamnonin sun bayyana rashin jin daɗinsu akan yanda siyasar jihar ke gudana. Shi yasa suke ganin ya dace su tattauna don warware matsalar cikin fahimtar juna.

Jihar Ribas dai ta PDP ce, kuma Wike shima ɗan PDP, sai dai a yanzu haka Minista ne a gwamnatin APC ta Tinubu.

Sai dai rikicin da ya kuma ɗaukar salo na tsige shugaban masu rinjaye na majalissar da kuma ƙone wani sashi na majalisar, gami da samar da kakakin majalissar har mutane biyu, su suka ƙara tabbatarwa gwamnonin dole su dubi lamarin kafin lokaci ya ƙurace.

Idan dai za a iya tunawa Wike shi ya jagoranci komai da komai don ganin gwamna Fubara ya zama gwamna a jihar mai arziƙin man fetur, in da ya yi nasarar zama gwamna ranar 18 ga watan Maris ɗin shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here