Babban Bankin Najeriya ya bayar da tabbacin wadatuwar takardun kuɗi

0
447

Babban bankin Najeriya ya sanar da ‘yan Najeriya tabbacin ba wata matsalar ƙarancin takardun kuɗi da za a fuskanta a ƙasar.

Hakan dai na zuwa ne yanda aka wayi gari a satin da suka wuce ana fuskantar ƙarancin ƙudi a wasu sassan na wasu manyan biranen Nijeriyar. Wuraren da kuɗaɗen suka fi karanci akwai injin cirar kuɗi na banki, sai masu wajen cirar kuɗi a shaguna da kuma wurin ‘yan canji.

A sanarwar da daraktan sadarwa na babban bankin ƙasar ya sakawa hannu, Isa AbdulMumin, ya bayyana cewar a binciken da suka yi sun gano yanda bankunan kasuwa suka kwashi kuɗaɗe masu yawa ne a manyan biranen ƙasar da har jama’a suka fara shiga matsi na ƙarancin takardun kuɗin idan sun je cira a banki ko shaguna.


Ya ƙara da cewar akwai takardun kuɗaɗe masu yawa da za su wadata a ƙasa baki ɗaya. Don haka fargaba da zullumin ba su da wani alfanu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here