Kowacce shiyya a Najeriya za ta tsira da gidaje dubu biyar – Minista T. Gwarzo

0
243

Gwamnatin tarayya za ta gina gidaje dubu 30 kyauta ga ƴan ƙasa

A ƙoƙarin gwannatin Najeriya na sauƙaƙawa al’umma matsalar muhalli da suke fama da ita, a yanzu ta fara shirin gina gidaje dubu biyar-biyar a dukkan shiyyoyi shida na ƙasa, wanda ya kama gidaje dubu talatin kenan baki ɗaya ƙasar.

Ƙaramin ministan gidaje da raya karkara na Najeriya, Alhaji Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ne ya sanar da hakan a wata zantawarsa da sashen Hausa na BBC dangane da bikin ranar inganta wuraren zama da gidaje na wannan shekara.

Ya kuma ƙara da cewa tun asali dama akwai wannan tsari na gina gidaje a ƙasar, amma kasancewar wannan ma’aikatar a baya tana ƙarƙashin ma’aikatar ayyuka da makamashi, sai aikin ya shiga wani yanayi. Amma yanzu an cire ta daga nan kuma za ta fara aiki gadan-gadan.

“Muna da shirin gina gidaje dubu dai-dai a kowacce jiha. Muna jiran shugaban ƙasa ya amince mana sai kawai mu ƙaddamar da aikin.

Ya kuma ce tsarin zai kasance waɗanda ba su da gata za’a basu kyauta, wasu kuma a ba su cikin farashi mai sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here