Ƴan bindiga sun yi awon gaba da Amarya da Uwargidan shugaban ƙaramar hukuma a Jigawa

0
473

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari gidan shugaban ƙaramar hukumar Kiyawa da ke jihar Jigawa tare da sace matansa guda biyu.

Shugaban ƙaramar hukumar Honarabul Nasiru Ahmed Kiyawa – wanda ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin – ya ce ‘yan bindigar sun je gidan nasa ne bayan sallar Isha’i a ranar Juma’a daddare, inda suka kore mutanen da ke kofar gidan nasa kafin su shiga ciki.

Ya ƙara da cewa “sau biyu suna harba bindiga a ƙofar gidana kafin su shigo ciki”.

Daga nan ne kuma suka tafi da matan nasa guda biyu, inda kuma har yanzu suke garkuwa da su, kamar yadda ya tabbatar wa BBC.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Lawan Adam Shiisu ya tabbatar wa BBC faruwar lamarain, inda ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ta samu kiran gaggawa kan lamarin, inda kuma nan take suka tura jami’ansu domin kai ɗauki.

Sai dai kafin zuwan jami’an na ‘yan sanda tuni ‘yan bindigar sun yi awon gaba da matan shugaban ƙaramar hukumar.

DSP Shiisu ya ce tuni rundunar ‘yan sanda jihar ta baza jami’an a lungu da saƙo na ƙaramar hukumar domin kuɓutar da matan.

Ya kuma ce rundunar ‘yan sandan na maraba da duk wasu bayanai da za su taimaka wajen kai ga gano masu garkuwan don kuɓutar da matan.

Matsalar garkuwa da mutane dai wani baƙon al’amari ne a jihar ta Jigawa, to sai dai matsalar na neman kunno kai cikin jihar a baya-bayan nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here