Mun yi farin ciki da hukuncin da kotu ta yi kan kujerar Gwamnan Kano – Ma’aikatan Kano

0
982

Wasu Ma’aikata a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun bayyana ra’ayinsu dangane da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ta yi na baiwa jamiyyar APC nasara a hukuncin da ta yanke game da zaɓen gwamnan jihar.

Ma’aikatan da su ka kasance malaman makarantun Firamare da ke su ke aiki a ƙarƙashin ma’aikatar ilimi sun bayyana haka ne a lokacin da su ke tattaunawa da Kano Times jim kaɗan da kotun ɗaukaka ƙarar ta sanar da hukuncin.

Nasiru Abdullahi (Ba sunansa na ainihi ba) ya bayyana cewa “Duk wani ma’aikaci da ka sani musamman malamin Firamare to yana murna da wannan hukuncin.”

“Wannan gwamnatin ta Abba Gida -Gida ta cire mana ƙarin albashin da ta tarar gwamnatin baya ta yi mana ba tare da wani dalili ba.”

Ibrahim Yusuf cewa ya yi “Muna murna sosai da wannan hukuncin kuma zamu cigaba da addu’a domin tabbatarsa a kotun ƙoli. Babban fatanmu shi ne ganin bayan wannan gwamnati ta NNPP da ba ta ƙaunar ma’aikat .”

Maryam Musa wacce ɗaya ce daga cikin ma’aikatan da gwamnatin Kano ta dakatar cewa ta yi sun yi farin ciki da wannan hukuncin kuma Allah ne ya amsa addu’ar su.

“Muna murna da hukuncin kotu kuma babu shakka addu’ar mu ce ta karɓu akan rashin adalcin da gwamnatin Abba ta yi mana”

Hakazalika ma’aikatan sun yi kira ga ƴanuwansu malaman makaranta da ke faɗin jihar Kano da su cigaba da addu’ar ganin jam’iyyar APC ta kuma samun nasara a kotun ƙoli.

A jiya juma’a ne kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a watan Maris din 2023.

A hukuncin da ta yanke, kotun ta amince da matsayar kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Kano, wadda ta ce ba a bi ƙa’ida ba wajen tsayar da Abba Kabir takara, saboda haka bai cancanci tsayawa takara a zaɓen na gwamna ba.

A ranar 20 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta jihar Kano ta ce Gawuna ne ya lashe zaɓen wanda aka gudanar a watan Maris.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here