Rundunar sojin Najeriya sun kuɓutar da wasu Yara da aka yi ƙoƙarin safararsu

0
427

Wata rundunar sojin Najeriya ta musamman da ke kula da jahohin Benuwe, Nasarawa da Taraba ta sanar da samun nasarar kuɓutar da wasu ƙananan yara da aka yi yunƙurin safararsu zuwa birnin tarayya Abuja.

A cewar babban kwamandan rundunar, Janar Sunday, ya bayyanawa manema labarai cewar, a ranar Laraba 20 ga watan Satumbar 2023 suka samu labaran sirri dangane da yunƙurin safarar yaran.

Dirarsu babbar tashar motar ta lafiya, suka yi sa’ar samun yaran, tare da wani matashi ɗan shekaru 17 da yake kula da su a motar.

A lokacin da suke tuhumar matashin mai suna Samuel, ya bayyana cewar daga Angwan-Kaɓir ta ƙaramar hukumar Shendam a jihar Filato suka sato yaran.

Sai dai sojin ba su samu damar kama matar da take tare da su ba. Domin hango su da ta yi ne, ya sa ta arce ta bar Samuel da yaran.

Ƙananan yaran da ba su wuce shekaru 2 zuwa biyar ba, sun ƙunshi Maza 2, Mata 3; akwai Nasiru, Apinan, Khairat, Izan, da kuma Adinan.

Tuni dai suka ci gaba da bincike don ganin sun kamo Madam Tina da ke zaune a garin Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here