Najeriya ta ce ta kafa kwamiti da niyyar rage tsadar iskar gas

0
267

Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwarta kan tsadar iskar gas a ƙasar, kuma ta kafa wani kwamiti da zai yi kokarin lalubo hanyoyin rage farashin gas nan da mako guda tare da magance matsalolin samar da shi a fadin kasar.

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Ekperikpe Ekpo ne ya yi wannan tsokaci a kan kalubalen da ke tattare da samar da man fetur da kuma farashin iskar gas a kasuwannin cikin gida.

Jaridar Daily Trust ta ambato Ekperikpe Ekpo na cewa matakin ya zama wajibi saboda ci gaba da karuwar farashi da iskar gas ke yi a watannin baya-bayan nan, inda ya kai sama da N900 a kan duk kilogiram daya, har ma ya haura N1,200 a wasu jihohin.

Ministan a cikin wata sanarwa, ya ce manyan kalubalen da aka gano da ke da haddasa karuwar farashin iskar gas sun hada da karancin samun canji kuɗaɗen waje domin sayo iskar gas da kuma ƙarancin kawo gas din kasuwanni Najeriya.

Ministan wanda ya bayyana cewa Najeriya na da arzikin iskar gas, ya ce yanayin da wasu kamfanoni na ƙasashen duniya suka fi damuwa da fitar da iskar gas ba tare da sadaukar da wani adadi mai yawa ga kasuwannin cikin gida ba, abu ne da ba za a amince da shi ba.

Bayan haka ministan ya kafa kwamitin karkashin jagorancin shugaban Hukumar Kula da Harkokin Albarkatun Man Fetur ta Kasa ta Najeriya NMDPRA tare da ba da umarnin fitar da shawarwari kan yadda za a bunƙasa samarwa da kuma tabbatar da ganin an rage farashin iskar gas cikin mako guda.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here