Kungiyar wa’azin musulunci ta Izala tayi Allah wadai da kisan kiyashi na harin wani jirgin sama da aka yiwa al’ummar musulmai a jahar kaduna yayin da suke gudanar da wani taro.
Shugaban kungiyar Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga gwamnantin tarayya da tayi bincike na gaskiya Akan hakikanin abun da ya faru, kuma ta hukunta masu hannu a cikin wannan lamari.
Lamarin de ya faru ne a kauyen Tudun Biri da ke gundumar Afaka a lardin Rigasa a karamar hukumar Igabi, inda aka yi kuskuren kashe musulman da suke gudanar da wani taro tare da jikkata wasu da dama biyo bayan wani hari da jirgin yaki mara matuki na soja ya kai don farautan ‘yan ta’ada.
Sheikh Bala Lau yayi jimami kwarai, ganin yadda daruruwan mutane suka rasa ransu a wannan lamari. A karshe yayi addu’ar Allah ya Jikan musulmai muminai, ya baiwa wadanda suka ji rauni lafiya, ya kuma kiyaye faruwar haka a gaba.
JIBWIS NIGERIA