By Salisu Ismail Kabuga
Basaraken gargajiya, Falakin Shinkafi, Ambassador Yunusa Hamza ya yi Allah wadai da harin da sojojin Nigeria suka kaiwa Mazauna kauyen Tudun-Biri yayin da suke tsaka da gudanar da taron Maulidin Annabi Muhammadu (s.a.w) wanda yayi sanadiyyar rasuwar mutane da dama da kuma samun raunika ga wasu.
A Lahadin da ta gabata ne, wani jirgin yakin sojin Nigeria ya yi ruwan bama-bamai akan Al’ummar Musulmai a kauyen Tudun-Biri dake Kaduna yayin da suke taron maulid wanda hakan ya janyo salwantar rayuwa da dama.
Rahotanni sun fayyace munin abinda ya faru da cewa har kawo yanzu ba’a samu tartibin yawan alkalumman wadan da suka rasu ba sakamakon harin wanda ya rutsa da Mata da Maza da kuma Kananan yara da Dattawa yayin da wasu da dama ke kwance a Asibiti cikin mawuyacin hali.
Sai dai kuma, daga bisani rudunar Sojin Nigeria ta futo karara ta bayyana faruwar lamarin a matsayin kuskure da nuna nadamar hakan.
Cikin wata sanarwa da ya futar a Larabar nan ga manema labaru, Falakin Shinkafi, ya bayyana alhini da kuma dangantaka abinda sojojin kusa aikata sakaci da nuna rashin kwarewa inda yace bai kamata a kauda Kai akan irin wadannan sakaci ba domin hakan ya zama izina nan gaba.
“Muna kira da kakkausar murya ga gwamnatin tarayya da masu fada aji a Arewacin Nigeria da su fito domin neman abi kadin abun da akayi na Kisan gillar da akayiwa bayin Allah nan da suke tsaka da gudanar da maulidin Annabi (S.A.W) a garin Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna,” cikin kalaman Falakin Shinkafi Ambassador Yunusa Hamza.
Basaraken ya kuma kara da cewa, “Babu shakka wannan al’amari abun Allah-wadai ne, amma akwai bukatar daukar matakai akan waɗanda suke da alhaki da Kuma kare faruwar hakan a nan gaba, Domin barin batun hakan nan zai sa a cigaba da kashe Mutane Babu gaira babu dalili.
…………………………………………….