Kano Times

Nothing but authentic

Cocin Katolika ta amince da auren jinsi

Fafaroma Francis ya ba da izini ga limaman Cocin Katolika su rika sa albarka ga ma’aurata masu auren jinsi, wadda nasara ce ga al’ummar nan ta LGBTQ+ da ke cikin Cocin Roman Katolika.

BBC ta ruwaito rahoton cewa jagoran Cocin Katolika na cewa, a wasu lokuta, ya kamata limaman coci su iya sa albarka ga ma’auratan da suka sauya jinsi da kuma waɗanda ke tsaka-tsaki.

Sai dai ya kara da cewa ana ci gaba da kallon aure a matsayin tsakanin mace da namiji.

A ranar Litinin ne Fafaroma Francis ya amince da wata takarda ta Vatican da ke bayyana matakin.

Ko da yake takardar da kanta ta ce dole ne limamai su tsayar da shawara bisa ga shari’a, Fadar Vatican ta ce ya kamata ya zama alamar cewa “Allah yana maraba da kowa.”

Cardinal Víctor Manuel Fernández, ɗaya daga cikin shugabannin cocin, yayin da yake gabatar da rubutun, ya bayyana ƙarara cewa matsayin da aka yi wa kwaskwarima bai ba da amincewar ma’auratan da ke cikin cocin Katolika a hukumance ba.

A cikin 2021, Fafaroma ya taɓa bayyanawa cewa an hana kiristoci sa albarka ga masu yin auren jinsi, yana mai nuni da imanin cewa Allah ba zai “albarkaci zunubi” ba.

A cikin Cocin Katolika, albarka ta ƙunshi addu’a ko roƙo, yana roƙon Allah ya ba da tagomashi ga mutum ko daidaikun waɗanda ke karɓar albarkar.

A watan Oktoba, Fafaroma Francis ya yi nuni da cewa watakila ya yarda ya ga ma’auratan maza da mata a Cocin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *