Kano Times

Nothing but authentic

Abba Gida – Gida ya yi bankwana da al’ummar jihar Kano – Salihu Tanko Yakasai

Tsohon Dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyar PRP a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana cewa hirar da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya yi a jiya Litinin a kafafen yaɗa labarai daban – daban alama ce ta bankwana da mulkin jihar gabanin hukuncin kotun ƙoli.

Salihu Tanko Yakasai wanda a yanzu shi ne mataimaki na musamman kan kafofin sadarwa na zamani ga shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bayyana hakan ne a safiyar yau Talata a shafinsa na Facebook.

Ya ce “Yai bankwana da matasa a filin Mahaha, jiya kuma yai bankwana da kanawa a gidajen rediyo. Saura a nemi gafarar yan rusau kafin a sauka, dan bayan hisabin duniya akwai na lahira.”

A jiya ne dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar jawabi na musamman ga al’ummar jihar Kano kai tsaye ta kafafen yada labarai.

Kafafen yaɗa labaran sun hada da: Radio Kano (AM/FM), ARTV, Tambari TV, Arewa Radio, Pyramid Radio, Freedom Radio, Premier Radio, Nasara Radio, Kwankwasiyya Reporters da kuma kamfanin dillancin labarai na ƙasa wato NAN.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *