Ba za mu yadda da ƙasa da naira dubu 200 a matsayin mafi karancin albashi ba – NLC

0
464

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC ta bayyana cewa ba za ta amince da ƙasa da naira dubu 200 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Shugaban NLC Joe Ajaero, ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da jaridar Vanguard da ke Najeriya.

Tun da farko an tambayi Kwamared Ajaero kan cewa a tattaunawarku ta ƙarshe da gwamnatin tarayya kun tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi, kun yi nazari kan alkaluman tattalin arziki, kun ce sabon albashin ba zai gaza N200,000 ba. Shin har yanzu kuna riƙe wannan matsayi ko akwai wani canji?

Sai ya bayar da amsa kamar haka” To, ba kawai na ce N200,000 ba. Na yi ƙoƙarin gano darajar Dala 200 a lokacin. Don haka, idan kana duban sauye-sauye akai-akai ta mahangar Dala dari biyu, za ka gane cewa Dala 200 ta kai kusan naira dubu dari biyu a yanzu. Dole ne gwamnati ta daidaita dangane da yanayin da ake ciki.

A shekarar 2018, majalisar wakilan Najeriya ta sa hannu kan kudirin dokar da ya tanadi a biya naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati na jiha da na tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here