Jami’an tsaro sun cafke wata ɓarauniyar yara a Kano

0
459

Jami’an tsaron aikin sa kai wato bijilanti, a jihar Kano sun kama wata mata da ake zargin mai satar mutane ce a unguwar sharada da ke yankin ƙaramar hukumar Birnin Kano da kewaye.

Gidan Rediyon Arewa ya rawaito cewa matar dai ta yaudari wata mata da ƴaƴan ta 4, maza 2 mata 2 da niyyar za ta kai su wani gida da ta ce ana bayar da taimakon kudi da kuma kayan abinci.

Rahoton ya ƙara da cewa hakan ne ya sa wasu ƴan bijilanti da ke sintiri a yankin suka yi ta fakon ta har Allah ya basu nasarar kama ta, wanda tuni ta yi cinikin duk namiji akan kuɗi Naira miliyan daya, mace kuma naira dubu ɗari takwas.

Kawo lokacin hada wannan rahoton jami’an tsaron sun mika matar da yaran da ta sato zuwa ga rundunar ƴan sandan Kano domin faɗaɗa bincike a cewar Babban Kwamandan bijilanti na Jihar kano Alhaji Shehu Rabi’u.

Ana samun matsalar satar ƙananan yara a jihar Kano inda ake safararsu zuwa kudancin Najeriya inda aka sayar da su tare da sauya musu addini.

Wasu na danganta batun ɓatan yaran da ake samu a jihar da sakacin iyayensu, amma wasu na da ra’ayin akwai sakacin hukumomi wajen tabbatar da doka da oda da kuma kare hakkin al’umma

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here