Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Muhammad Rabi’u Musa Rijiyar Lemo ya bayyana cewa maganganun da Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ke yi game da hadisan Manzon Allah S.A.W na da haɗarin gaske.
Sheikh Musa Rijiyar ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis kamar yadda jaridar Kano Times ta gani.
Rubutun mai taken “Dr. Ahmad Gumi Da Sunnar Annabi” ya yi tsokaci kan Sheikh Ahmad Gumi din.
Ga Rubutun kamar haka
Dr Ahmad Gumi Da Sunnar Annabi!!.
Maganganun Dr Ahmad Gumi akan hadisan Manzon Allah S.A.W maganganu ne masu hadarin gaske ga musulunci da musulmai, domin rushe hadisai ne gaba daya, da sa wa musulmai shakku a kansu, da budewa makiya sunnah da yan kala kato da yan boko akida kofar ci gaba da barna a musulunci.
Wani abin da yake bayyane ga daliban ilimi da malamai Dr Ahmad Gumi ya yi hannun riga da ilimin addini, inda ilimi ya yi daban, inda shi kuma ya yi daban. Don babu yadda za a yi mai ilimi ko dalibin ilimi ya siffata littafan hadisi ingantattu, kamar Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da buhun yashi, wanda ake tsintar kwayar shinkafa daya daya a cikinsa, saboda fadin haka sabawa malamai ne gabadaya da suka hadu a kan ingancin wadannan littattafai da aiki da su. Wani abin da yake kara tabbatar da haka shi ne, yabon wasu littattafai wadanda marubutansu sun dogara ne a kan wadancan littattafan da ya kushe, kuma ma’abotansu sun zo bayan shudewar ma’abota wadancan littattafai na hadisi. Tufka da warwara dai kawai hade da jahilci da sunan ilimi.
Wata magana ta Dr Gumi da take kara tabbatar da nisan sa ga ilimi cewa : Wai da Imamu Malik ya rayu da ya rushe Muwadda!!. To abin tambaya a nan ; Me ya sa Dr yake karantar da ita?. Kuma idan ya rushe ta, da me zai yi aiki?!. Zai daina aiki ne da hadisai ko ya zai yi?!.
Gaskiyar magana Dr Ahmad Gumi ya zama jarraba ga Sunnah da Ahlussunnah a wannan zamani, kuma WALLAHI barnar da yake yadawa da sunan ilimi da gyara ta fi amfanin da yake raya cewa yana kawowa.
Fatanmu Allah ya shirye shi, ko ya yi mana maganinsa.
Leave a Reply