Kano Times

January 21, 2026

Gwamnan Kano ya kori kwamishina kan kalaman ‘tunzura al’umma

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sallami kwamishinan filaye da safiyo na gwamnatin jihar, Adamu Aliyu Kibiya daga muĆ™aminsa, bayan zargin sa da furta kalaman tunzura al’umma.

Bugu da ƙari sallamar ta shafi mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin wasanni da matasa,Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Boye wanda shi ma ake zargi da furta kalaman da ba su dace ba a madadin gwamnatin.

A Ć™arshen makon nan ne bidiyon jami’an gwamnatin suka rinĆ™a yawo a shafukan sada zumunta, inda suke furta kalamai game da shari’ar da ake yi kan zaÉ“en gwamnan jihar da ya gabata.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaÉ—a labarai na jihar, Baba Halilu ĆŠantiye da kuma na shari’a Haruna Isa Dederi suka karanta a daren ranar Alhamis, sun ce jami’an gwamnatin sun yi magana ba tare da izinin gwamna ba, sun kuma yi kalamai na tunzura al’umma sannan kuma sun ci zarafin mataimakin shugaban Ć™asar, Kashin Shettima.

A cikin kwanakin nan dai yanayin na siyasa ya ƙara zafafa gabanin hukuncin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna na jihar.

Manyan jam’iyyu a jihar, NNPP da APC sun gudanar da addu’o’i da azumi domin neman nasara a shari’ar.

A baya dai É—aya daga cikin alĆ™alan kotun ta yi zargin cewa akwai wasu da ke yunĆ™urin bai wa alĆ™alai da lauyoyin kotun cin hanci domin samun nasara a shari’ar.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top