Wasu mutanen na ta kururuwar cewa wai addu’ar mutanen da aka zalunta – masu shaguna a masallacin Eid ce ta karbu. Shi ya sa Abba ya faÉ—i a court!
Da farko, ba na fariciki da asarar dukiya da mutane suka yi. Sannan a ra’ayina, mutanen da suka yi gini a cikin makarantu da maÆ™abartu su suka fi cancanta na a rushewa gidaje akan Æ´an kasuwa. But kowace gwamnati na da nata tunanin. Na yi post akan wannan a baya.
But mu duba tarihi akan rusau da zaluncin gwamnati a Nigeria.
1) Ganduje yayi mulki a Kano na 8 years. Babu wanda zai ce shi mulkin sahabbai yayi babu mutum ko É—aya da ya zalunta. In summary, Ganduje ya rushewa mutane gidaje sama da 160 a Hajj Camp ya gina shagunan neman kuÉ—i. Mutane suna kuka aka fitar da su daga gidajensu. Haka masu pension da gratuity na tsawon shekaru masu yawa. Haka suka rinqa mutuwa ba tare da an biya su haƙƙinsu ba. Ga ma’aikatan da aka ringa yankewa albashi duk wata. Ga mutanen da suke sana’oi a inda suke zaune aka siyarwa da Æ´an kasuwa filayen. Hatta a Æ´an siyasa Æ´an APC da dama Ganduje ya zalunce su a harkar takara. Ƴan tsirari ne suka ji daÉ—in gwamnatinshi a Kano. Duka waÉ—annan mutanen sun yi masa muguwar addu’a da tsinuwa kala-kala. But Ganduje still gaba yake ci a wajen wasu. Shin anan za mu ce Allah be karÉ“i addua’rsu ba ko kuma Allah ya karÉ“a amma ya yiwa Ganduje talala ne?
2) El-Rufa’i da yana Ministan Abuja yayi rusau na tashin hankali. Mutane da yawa sun talauce sun tsiyace. Sun yi masa muguwar addu’a. Amma haka yayi ta yin muÆ™amai kala-kala bayan ya gama ministan. Shin su ina maganar addu’ar su? Ko ita addu’a irinsu Abba Kabir kawai take ci saboda É—an Kwankwasiyya ne?
3) El-Rufa’i ya tsaya takarar gwamna a Kaduna. Ya ci zango na farko. Kowa ya san Kasuwar Bacci me rumfuna da shaguna dubunnai. Amma haka El-Rufa’i ya je ya rushewa mutane dukiyarsu. Mutane suka talauce. Babu irin tsinuwa da addu’ar da ba su yi ba. Duk da haka, El-Rufa’i ya kuma tsayawa takara zango na biyu, ga addu’ar masu rusau amma Allah ya ba shi nasara. Shi addu’a ba ta cin shi ne? Ko saboda É—an APC ne?
4) El-Rufa’i ya tsayar da Uba Sani takara, duk da zaluntar talakawa bayin Allah da yayi, amma haka shi ma yaci. But don’t forget that El-Rufa’i da Ganduje duk Æ´an APC ne. Shin su Æ´an APC addu’ar mutanen da suka zalunta ba ta aiki akansu ne? Don’t get me wrong. Ba ina nufin Allah ba ya karÉ“ar addu’ar talakawa akan shugabanni ba ne, I’m not Atiku Abubakar. Ina fito mana da abubuwa fili don masu basira su fahimta.
5) Ga Bola Ahmad Tinubu, tun da ya fara mulki a Lagos yake rushe areas É—in talakawa yana gina sabbin gurare. Haka duk gwamnonin da suka biyo bayanshi suka ci gaba da dabbaÆ™a wannan sunnar har zuwa yau. Kar ku manta da Hausawanmu Mazauna Lagos masu sana’ar achaÉ“a. Kowa yaga yadda aka Æ™wace musu baburansu. Aka kuma kama su. A Æ™arshe aka kore su daga garin. Lauyoyi har daga Kano sun je Lagos don basu kariya. Babu irin addu’ar da ba su yi ba saboda zaluntarsu da aka yi. Yanzu ga Bola Tinubu ya zama shugaban Æ™asa. Duk da cewa yana cikin jerin mutanen da ake zarginsu da kashe É—aruruwan rayukan Hausawa mazauna Lagos a wani rikici da aka yi somewhere in 2002/2004. Sheikh Ja’afar a mimbarin Juma’a ya kama sunayensu ya tsine musu albarka. Shin ya batun addu’oin da aka yi musu? Ko don shi ma ya shiga APC addu’a ba ta cin su instantly?
6) Ga Isra’ila nan, tun da aka kafa ta a 1945 take rushe gidaje da unguwannin FalasÉ—inawa ta na Æ™ara faÉ—aÉ—a Æ™asarta. Musulman duniya kullum addu’a suke Allah ya karya Isra’ila da magoya bayanta. Yanzu saboda Isra’ila ba ta karye ba sai mu ce akan daidai take duk da addu’oin da muke yi? Allah is not a Greek God of ANGER (Zeus).
A Æ™arshe, wai wane saÆ™o na ke son fitowa da shi nan? Su shugabanni Allah na musu lamuni ko da kuwa akwai zalunci a gudanarwarsu. Sannan ita addu’a akan shugaba ba wai sai ta zama instant ba ne ta ke cika addu’a. Wata addu’ar sai a Lahira Allah zai yiwa mutum sakayya. Sannan su shugabanni suna da wata kariya ta musamman daga wajen Allah. Imagine duk addu’ar da mutane za su yi akan shugabanni Allah zai amsa ya kuma yanke musu hukunci da ita nan take, da babu shugaban da zai yi kwana É—aya akan kujerar mulki.
Anan za mu fahimci cewa ba gaskiya ba ne cewa addu’ar mutanen da aka rusawa shaguna ce ta kama Abba. Saboda al’amari ne na gaibu. Babu wanda Allah ya cewa addu’ar masu rusau ce ta karÉ“u. Ko da wani malamin duba ko tsibbu ya faÉ—i haka to wallahi Æ™arya yake. Misalan da na kawo a sama sun ishi duk me basira Mu ringa faÉ—aÉ—a tunani kafin mu yi magana, please. However, idan kuma addu’ar ce ta karÉ“u, this means that Allah na son Abba da alkhairi. Don ga shi tun ba aje ko’ina ba Allah ya É—auki fansa akan abun da ya yi. Shi kuma Ganduje da ya ke zalunci da mugunta but kullum wasu kallon gaba yake yi shin ba za mu ce istidraji Allah ya ke masa ba? Ka san istidraji kuwa?
Aisar Fagge Malami ne a Kwalejin Fasaha da ke Kano