Shinkafa ‘yar Sarki ce. Tun zamanin Obasanjo ake so a dakile shigo da ita saboda wai ana tafka asara wajen shigo da ita. A lokacin Ƴar Adua an bayar da lokaci zuwa kafin a hana shigo da ita. Mutuwar Shugaba ‘Yar Adua da hawan Jonathan ya sa aka dage shirin zuwa wani lokaci.
Daga hawan Shugaba Buhari a 2015, sai aka gudanar da hana bayar da canji ga wasu kayayyaki 41, daga bisani kuma aka ƙara wasu abubuwan suka zama 43.
Wadannan kayayyaki ba a hana shigo da su ba, amma kuma duk mai shigo da su ba zai samu canjin dala a hannun gwamnati ba sai ta bayan fage. Shinkafa ita ce lambawan.
A shekarar 2016, sai gwamnati ta hana shigo da shinkafa ta bodojin kasa sai ta ruwa. Kuma aka mai da harajin shigo da ita zuwa kashi 70 na ainihin abin da aka sayo ta.
A shekarar 2018, sai aka matsantawa. Gwamnati ta daina ba wa masu shigo da shinkafa form din da ake kira Form M da yake ba da damar dauko kaya a shigo da su. Wannan kuma ya sa farashin shinkafar ya kara zabura.
Daga nan kuma a cikin 2019, haka zikau gwamnati ta garkame boda ta hana shigo da komai wai domin a hana fasa kauri da sauran abubuwa. Aka ce duk wanda ya dauko shinkafa a bindige shi. Allah ne kadai ya san adadin rayukan da aka hallaka saboda shinkafa.
A watan Janairu na 2022 sai gwamnati ta hana shigo da shinkafa ta tasoshin jiragen ruwa.
Akan wannan matakin ake har yanzu da aka ce an sakarwa masu son shigo da ita mara za su iya samun canji daga hukuma.
Sai dai fa hakan ba zai yiwu ba har sai an bayar da dama a shigo da ita din ta tasoshin jiragen ruwa ko na sama ko kuma ta bodojin kasa.
Akwai wani kalubalen kuma. A watan Agustan shekarar nan, gwamnatin Indiya ta hana fitar da shinkafa zuwa kasashen waje saboda su ma ba ta isar su a cewar su. Sai dai Thailand ta ce wannan dama ce gare ta na samar da shinkafa mai yawa ga kasashen waje musamman Afrika.
Hana shigo da shinkafa Nijeriya ya taimaka wajen samar da kamfanonin gida da ke samar da ita kuma suke samun gagarumar riba mara misali a daidai lokacin da farashinta ke hauhawa kamar gishirin andurus.
Idan aka ce za a iya shigo da ita, akwai yiwuwar ba za ta canja zani ba saboda canjin dala da kuma yadda ‘yan kasuwa ke hade kansu suna gallazawa jama’a ba tare da gwamnati ta ce kanzil ba. Ta yiwu kuma kudin haraji na babu gaira ya taka rawa wajen hana saukowar abubuwan nan 43 da aka sakar wa mara.
Bayan wadannan ababe 43, akwai wasu da dama da aka yi ta hana shigo da su kamar Taki da Motoci da sauransu.
Mafita gare mu na Rabbana.
Danladi Z. Haruna