Duniya Makwantar Rikici: Kwanaki Biyar da Fara Yaƙin Isra’ila

0
178

JIYA Alhamis, sakataren harkokin kasashen waje na Amurka, Anthony Blinken ya ziyarci kasar Israila. Ya je ziyarar ne domin gabatar da sakon shugaban kasar Amurka Joe Biden a madadin sauran Amurkawa dangane da yakin da ake yi a tsakanin Palasdinawa da Yahudawa. Yau da safe Juma’a, ministan harkokin tsaro na Amurka Lyold Austin, ya sauka a birnin Tel Aviv na kasar Israila. Shima yaje Israeli da nasa sakon.

Da Blinken ya je Israila jiya, a filin taro ya gaya wa Firaminista Benjamin Netanyahu cewa, ya zo Israila ne a matsayin wakilcin Amurka, sannan kuma a matsayinsa na Bayahude Usul. Sannan sakon da yake tafe da shi, shi ne. “The message that I bring to Israel is this: You may be strong enough on your own to defend yourself, but as long as America exists, you will never, ever have to. We will always be there by your side.” “Abin da nake tafe da shi gareku: ku sani, kuna da karfin da zaku iya kare kasarku, muddin Amurka tana kan doron duniya, baku da fargaba. Duk rintsi muna bayanku.” A takaice dai da hannun Amurka a duk wani mataki da Israila ta shirya dauka.

Ilai, kuwa kamar yadda suka dauki alkawari, kwana uku kacal da fara yin wannan yakin, kasar Amurka ta girke jirgin ruwan nan na USS GERALD R FORD a tafkin Mediterranean, karon farko a tarihin Amurka. Wannan jirgin ruwan yana da filin da zai dauki jiragen saman yaki guda 75 akalla kafin a kera shi an kashe DALA biliyan 13. Bayan ziyarar sakataren harkokin kasashen waje Anthony Blinken domin karfafa diflomasiyya, shi kuma sakataren harkokin tsaro Lyold Austin yaje ne domin baiwa Israila duk wani agaji na tsaro da take bukata. Daga 1948 zuwa yanzu Amurka ta baiwa Israila taimakon kudi Sama da dala biliyan 236. Akwai Yahudawa a Amurka kusan miliyan shida, da Musulmi akalla miliyan hudu.

Bayan kaiwa Israeli farmakin ranar Asabat shirin da Yahudawa suka yi akan Palasdinawa a karkashin Israel Defense Forces, shi ne, su hallaka duk wani bil adama Musulmi da ke yankin GAZA. Su rushe duk wani gini da duk wata harka, su shafe GAZA daga doron kasa. Sannan su hana duk wani sha’anin addinin Musulunci a Masallacin Qudus as Sharif.

A matakan farko da suka fara dauka, shi ne sun katse wutar lantarki da ruwan famfo da guraren sarrafa makamashi girki da gas da duk wata iyakar da za a shiga da abinci ko abin sha. Haka sun dauki matakin kaiwa Palasdinawa hari a ko ina. Zuwa jiya Alhamis sun harba rokoki sama da dubu biyar. Sun kashe sama da mutum dubu biyu. Sun jikkata akalla mutum dubu hudu. Komai na harkar agaji da taimakon gaggawa na asibiti ya tsaya cik, mutane suna ta mutuwa.

Idan sun kammala hari da jiragen yaki, Israila ta shirya za ta mamaye GAZA da rundunar sojan kasa mutum dubu 165. Yau da asuba, wakilan majalisar dinkin duniya da suke aikin agaji a GAZA sun samu sanarwar daga jami’an sojin Israeli cewa duk wani mahaluki a GAZA an bashi awa 24 ya fice ya koma yankin kudancin Gazan. Duk wanda bai ji wannan gargadin ba, ko menene ya faru shi ya saya. Akwai akalla mutum miliyan daya da rabi da wannan umarnin ya shafa. Burin Israila su shiga, su yi yakin kare dangi a GAZA wato Genocide.

Yankin Palasdinu na Musulmi NE. GAZA ta Musulmi CE. West Bank na Musulmi NE.Baitil Maqdis na Musulmi NE. Hamas Musulmi ne da aka yi zabe halastacce suka kafa mulkin dimokuradiyya. Mu Musulmi muna goyon bayan Palasdinu su zauna a kasarsu. Muna Allah wadarai da Amurka da kawayenta. A gurinmu Israila azzaluma ce. Zalunci kuma haramun ne
Wannan hoton Blinken ne da Netanyahu jiya a Israeli

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here