
Fitaccen dan jaridar nan da ke aiki da tashar rediyo ta Freedom Radio da ke jihar Kano, Nasiru Salisu Zango ya shawarci gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da ya sauya shawara kan kuduinsa ma mika sunan Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso gaban majalisar dokokin jihar a matsayin ɗaya daga cikin Wanda zai naɗa kwamishina.
Nasiru Zango ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a yau Talata da mai taken ‘Gyara Kayan Ka’.
Ga Rubutun da Nasiru Zango ya yi kamar haka:
“Bayyana sunan Mustapha Kwankwaso a matsayin wanda za a naɗa kwamishina a Kano babban kuskure ne da zai ɗauki lokaci yana jawowa gwamnatin Kano da ɗarikar Kwankwasiyya surutai.
Ban ga dalilin yin wannan yar cikin gida ba, la‘akari da irin kurarin da ake ganin gwamnati me ci nayi na cewar zata bambamta da gwamnatin Ganduje dake shigar da yayan ta cikin tafiyar da gwamnati.
Akwai mutane da dama da suka wahaltawa gwamnati zahiran wa badinan amma an tsallake su an dauko dan lele za‘a nadashi kwamishina wannan tsantsar kaucewa abin da ake fadawa Al’ummar Kano ne kafin hawa gwamnati.
A matsayi na na wanda ba komai ba wato wa gairahum latajaru au ta jaru Ina baiwa gwamnan Kano shawara ya sauya wannan aniya tasa domin wallahi kuskure ne wanda kaf masoyan gwamna babu wanda yayi zaton haka za ta faru a irin gwamnatin da aka ce za a yi.
Yaushe ne kuma a ka fara halarta mulkin daga kwauri sai gwiwa a jihar Kano? To Ashe dama Ganduje da ya shigar da yayan sa gwamnati ba laifi yayi ba?
Karfa tun kafin tafiyar tayi nisa azo a fara tagumi idan ba kuka ba tumami.
Ni dai Nasiru Zango Dan Kano ban goyi bayan wannan son kai ba, ina kuma rokon a sake dubawa domin Kar a zo ana cewa kowannne Gauta Ja ne, kuma ayi amfani da balagaggiyar Hausa azo Ana cewa abin dake gidan Kaura shi ne a gidan Goje.
Dan Allah masu lissafi su taya ni lissafawa mu duba mu ajiye son rai mu fadawa kan mu Gaskiya.
Asha ruwa lafiya.”