A ko da yaushe in ka fita zuwa kasuwa za ka lura duk wata babbar hanya da za ta sada ka da wata babbar kasuwa a Kano, sai ka ga ma’aikata kala-kala suna rige-rigen kama direbobi da suka ɗauko kwastomomi, da suka shigo Kano da niyyar siyan kaya
Har ta kai yanzu direbobi da yawa sun ma fara haƙura da ɗauko fasinjoji ƴan kasuwa zuwa Kano, saboda tsangwama da rashin tsari da ake yi a cikin birnin Kano. Matsin ya yi yawa, a duk garin da direbobi ke tsoron shiga, musamman garin Kasuwanci kamar Kano, to tilas ciniki ya ja baya. Ɗaya daga cikin hanyoyin sanya takunkumi a gari da kuma durƙusar da kowani garin kasuwanci shi ne rashin aminci ga direbobi da fasinjoji masu siyan kaya.
Wani abun haushi kuma za ka ga da yamma nan ma ma’aikata sun kafa sun tsare suna ta kama motocin kayan da aka siya a kasuwannin Kano, kai tsaye fa ba direbobin ake wa illa ba kasuwar Kano, da ƴan kasuwa da kasuwancin Kano ake durƙusarwa.
Kwastomomi da yawa ma, sun haƙura sun daina shigowa Kano, sai Legas, Aba da sauransu ke zuwa saro kaya.
Lallai Gwamnatin Kano yakamata ta sake tsari, don kar nan gaba, mu ce wani ne ya yi mana illa, ko mu zargi ƙabilanci ko siyasa. Mu sani mu ne mu ka durƙusar da kasuwancinmu da kan mu.
In kuma wani tsari ne Gwamnatin Kano ta ɗauko na ƙoƙarin hana kasuwanci a Kano, to yakamata a faɗawa al’ummar Kano don kowa ya san nayi.
Wannan tsarin tsangwama da kyara ya faro ne tun daga tenure Kwankwaso ta biyu, Ganduje ya ɗora daga nan, ga shi a mulkin Abba ba ta canza zani ba, kai abun ma ya ƙara ta’azzara ne. Lallai ne Ƴan Kasuwa da shugabannin Kasuwa su miƙe don a gyara, ko kuma a durƙushe gaba ɗaya.
Mukhtar Mudi Sipikin