Kayan Masarufi sun yi tashin gwauran zabi gabanin bukin kirsimeti a kasuwanin cikin garin Kaduna kamar yadda gidan rediyo Najeriya Kaduna ya rawaito.
Mallam Abdulrahman Mai Provisions, ya bayyana cewa suna sayar da buhun shinkafa naira dubu arba’in da biyar amma yanzu ta kai dubu hamsin, inda aka samu karin dubu biyar, haka kuma sukari da filawa da kuma man gyaɗa suma an samu ƙarin naira dubu biyar akan watan da ya gabata.
Kabiru Mohammed direban mota ne dake daukar fasinja zuwa wasu garuru, ya bayyana cewa ƙarancin matafiya, wanda ya alaƙanta hakan da yanayi na tsadar man fetur inda ya ƙara da cewa kuɗin mota ya na nan yadda suka saba.
Wasu al’umma dake cikin garin Kaduna sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samo wasu hanyoyi da za’a rage raddadin cire tallafin man fetur da ya jawo tsadar kayan Masarufi domin su sami yin bikin kirsimeti cikin walwala.