Shugabanci a Najeriya: Yadda Yake da Yadda Muke Tunaninsa

0
214

Da alamu mutane da dama kallon shugabancin kungiya ko na shagon kasuwa suke yiwa shugabancin kasa ko na jiha. Wasu ma kallon shugabancin gidansu suke yiwa shugabanci kasa ko na jiha. Wasu kuma gani suke shugaban kasa ko gwabna shine doka shine oda, zai iya yin komai akan kowa a kuma sanda yaga dama ba wani tsari ko ka’ida da ya kamata ya bi. Wasu kuma gani suke yadda muke da lokacin bibiyar social media da jaridu da gidajen rediyo shima shugaban kasa ko gwabna haka yake da wannan yalwar lokacin saboda haka yasan kowanne zargi da ake akan kowanne jami’insa. Wasu ma gani suke idan wani jami’in gwabnati yana ta gina gidaje da siyan filaye a unguwarsu ai shikenan shugaban kasa ko gwabna ya sani. Toh gaskiya ba haka abun yake ba.

Shugabancin kasa ko jiha a kasa irin Najeriya da irin tsarin shugabancin mu, abu ne mai fadi da sarkakiya sosai. Sannan kuma mun kammama shugabannin mu da yawa tare da gina musu katangu masu tsayi sosai ba wai tsakaninsu da al’umma kadai ba, har ma tsakaninsu da sauran manya da kananan jami’an gwabnati. Sannan gwabnatin mu suna da fadi sosai da suke dauke da daruruwan ma’aikatu (MDAs). Kuma a MDA daya ma, kamar a bangaren lafiya da ilimi, za ka iya samun daruruwan maaikatu a karkashin ta (misali SUBEB, HMB da KSSMB a matakin jaha). Wannan yasa samun cikakken kulawa da bibiya a gwabnati daga bangaren gwabna ko shugaban kasa yake da mutukar wahala.

Na ji dadi sa’anninmu da ma na kasa da mu, da muka kware wajen iya sukar shugabanni, sun fara taka matakin shugabanci yadda za mu ga hakikanin yadda shugabanci yake a Najeriya da kuma irin sarkakiyarsa da wahalarsa musamman ga wanda yake son kwatanta gaskiya da rikon amana.

A misali, idan aka baka shugabancin wata ma’aikata a jiha ko tarayya wallahi za ka iya shafe shekara ba ka iya ganin gwabna ko shugaban kasa ba. Saboda haka duk inda ka kai da kishin aiki idan kana bukatar tallafawar gwabna ko shugaban kasa, idan mutanen fada na gewaye da su basu so ka ganshi ba, to wallahi in zaka shekara kana neman appointment ba zaka samu ganinsa ba. Sannan idan kwamishinan ka ko ministan ka ba mai kishi da son aiki bane irinka, in zaka tura memo sau dubu in yaga dama ba zai bari taje majalisar zartawa ba.

Idan kuma mai laifi ne kai kuma ma’aikatar ka mai generating kudi ce, to idan ka siye mutanen fada ka ringa buda musu ana ci da su, to duk wani zargi ko petition da za’a yi a kanka ba za su bari ya kai ga teburin gwabna ko shugaban kasa ba. Kuma da sunga wani abu da ya shafe ka ma zasu sanar da kai don ka gyara taku. Kuma ko shugaban ne ya jiyo wani abu a kanka a wani gurin za su yi iya bakin kokarinsu su wanke ka, su ce sharrin yanadawa ne da sauransu. Sannan kuma duk jami’an gwabnati masu barna sun san duk yadda za su bi su siye duk wani da suka san yana da tasiri akan shugaban kamar iyaye, malaman sa da manyan aminansa dss.

To a irin wannan yanayin fa duk wani shugaban kasa ko gwabna ko shugaban wata ma’aikata yake aiki a Najeriya. Kuma ya kamata musan cewa shi fa shugaban kasa ko gwabna da idonsa da kunnuwansa da bulalar dake hannunsa duk wasu ma’aikatun gwabnatin ne. Da su yake dogara wajen ji da gani da ma tsawatarwa ko ma kai duka idan anyi laifi. Iya ingancin wadannan ma’aikatun, iya yadda shugaban kasa zai ji ya gani kuma yayi hukunci yadda ya kamata.

Isah Mansur ya rubuto daga Kano – Najeriya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here