Duniya Makwantar Rikici: Tarihin Ƙungiyar Hamas

0
632

Kungiyar Hamas ta samo asali daga Kungiyar Ikhwanul Muslimun ta kasar Masar.

A shekara ta 1935, Kungiyar Ikhwan karkashin jagorancin Hassan Albanna ta fara gudanar da tuntuba a yankin Falasdinu da nufin kafa reshenta a yankin. Bayan tattaunawa da matasa da dalibai wanda ya dauki shekaru, an kafa reshen Kungiyar na farko a shekarar 1945 a birnin Qudus. Kuma a ranar 25 ga watan Nuwamba, 1956 an bude babban ofishin Kungiyar a birnin Gazza.

Bayan sama da shekaru 60 tana gudanar da ayyukanta a matsayin reshe na Kungiyar Ikhwan da cibiyarta take a kasar Masar, Kungiyar Hamas ta yi shelar tsinke alakarta da Ikhwan a shekara ta 2017 don ta samu damar ci gaba da aikinta na jihadi da cikakken yanci.

Ana daukar Sheikh Ahmad Yasin a matsayin wanda ya assasa Kungiyar Hamas. Daga cikin sanannun shugabannita akwai Khalid Mish’al wanda ya dade yana jagorantar bangaren Kungiyar na siyasa, da Yahya Sinwar da Abdul Aziz Rantisi da Ismail Haniyya.

Kungiyar Hamas tana da bangarori biyu: bangaren siyasa wanda yake shiga zabe a majalisar kasa ta Falasdinu da bangaren soji da suke kira da sunan Bataliyar Izzuddeen Alqassam, wanda sunan wani dakare ne da ya fara kaddamar da gwagwarmaya da makami a kan daular Bani Yahudu tun farkon kafa ta. Wannan sashe na Hamas shi ke kaddamar da aikin jihadi a kan kasar Israila, ciki har da yakin da ake ciki yanzu wanda aka yi wa lakabi da Ambaliyar Aqsa.

Bangaren Hamas na siyasa yana tafiyar da al’amuransa a bayyane, sabanin Bataliyar Izzuddeen Alqassam wacce take tafiyar da ayyukanta a sirri. A yau shi ke mulkin Zirin Gaza kuma yana cikin siyasar daular Falasdinu mai kwaryakwaryan cin gashin kai. Yana cikin wannan siyasa tsundum kuma a majalisar kasa ta Falasdinu shi ya fi ko wace kungiya da jamiyya yawan wakilai, ciki har da Kungiyar Fatah ta Shugaba Mahmoud Abbas.

Babu takamaimai dangane da adadin mayakan Hamas, amma majiyoyi da yawa suna nuni da cewa Kungiyar tana da zaratan mayaka kimanin 15,000 banda wasu daban da ake iya kira su dauki makami idan bukata ta gitta.

Hamas ta mallaki makamai nau’i dabam-daban, musamman rokoki masu cin zango mai nisa da matsakaici da manyan bindigogi da kananan jirage da ake sarrafawa daga nesa da kuma abinda ta ba Israila mamaki da shi a wannan yakin, watau baburan sama masu daukar mayaka kuma su yiwa na’ura mai hangen jiragen sama (radar) layar zana.

Babbar manufar Kungiyar Hamas ita ce yanta kafatanin kasar Falasdinu da fito-na-fito ta manufar Sahyuniyya ta kwacen kasa da kore Falasdinawa daga kasarsu ta gado. Wani abu muhimmi da ya kamata a fadi a nan shi ne, Kungiyar Hamas tana kaddamar da ayyukanta na jihadi ne kawai a cikin kasar Israila. Ba ta kai hari ga kowa a wajen kasar Yahudawa wadanda da su ne kawai take rigima, domin su ne suka kwace kasarta.

Kamar yadda mai karatu zai yi zato, wasu manyan kasashen duniya suna daukar Hamas a matsayin Kungiyar ta’addanci. Wadan nan kasashe sun hada da babbar algunguma kasar Amurka da Buritaniya da Tarayyar Kasashen Turai da Japan da Usturaliya, da sauransu.

Daga Farfesa Umar Labdo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here