Yau ta ke Ranar Matan Karkara ta Duniya

0
209

Ranar 15 ga watan Oktobar kowace shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar matan Karkara domin yin Nazari akan rayuwar su da kuma matsalolin da suke fuskanta.

An kebe wannan ranar ce domin tunawa da irin gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arziƙin al’ummomi a yankunan karkara d amata ke bayarwa.

Karfafawa matan karkara gwiwa na da matukar muhimmanci wajen kawar da yunwa da talauci a tsakanin al’umma in ji tsohon skaatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. 

A shekarar 2012, ne aka kaddamar da wannan rana wadda aka sauyawa suna daga ranar manoma mata ta duniya zuwa ranar matan karkara ta duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani shiri a baya bayan nan na karfafa matan karkara da kuma karfafa samar da abinci.

A cikin kowacce al’umma, matan karakara na taka muhimmiyar rawa wajen binkasa tattalin arziki musamman a kasashe masu tasowa.

Yawancin matan karkara kan shiga aikin noma ta yadda za su noma abinci da kuma samar da ababan more rayuwa.

Kazalika mata na taka muhimmiyar rawa ta fannin ilimi yara, da kula da marassalafiya da kuma tsofaffi, a don haka ba su gudunmuwar da ta dace zai matukar taimaka musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here