Mai Shari’a Dije Aboki ta yi wa fursinoni 13 afuwa a Kano

0
305

Babbar Alƙaliyar jihar Kano Mai Shari’a Dije Aboki ta yi wa fursinoni 13 daga gidajen kurkuku uku dake jihar afuwa.

Daga cikin fursinonin da aka yi wa afuwa akwai wasu daga gidajen ladabtarwa na yara da ke unguwar Goron Dutse da ke birnin Kano.

Dije ta yi wa fursinonin afuwa yayin da ita da wasu alkalai, lauyoyi, ‘yan sanda da dai sauran su suka ziyarci gidajen yarin Goron Dutse, Kurmawa da kuma gidan ladabtarwa dake jihar.

Kakakin ma’aikatar shari’a ta jihar, Baba Jibo, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ya ce Dije ta ta yi amfani da dama da doka ta ba ta ne yayin aikata haka.

Ya ce sai da Dije ta sake duba shari’ar fursinoni 13 yayin da ta ziyarci gidajen yarin kafin aka sake su.

Hakazalika Baba Jibo ya ce mai Shari’a Dije ta umarci sauran alkalai da su bayar da belin ko su saurari shari’ar sauran fursinonin dake tsare a gidajen yarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here