Tsawon shekaru sama da 20 a siyasar Kano, Kanawa na shan gware, ana ta kwallo damu tsàkanin manyan ‘yan siyasa uku: Kwankwaso, Shekarau da Ganduje. Yanayin siyasar mu da kuma gwanintar yaudara ta wadannan ‘yan siyasa, ya sa ana ci gaba da raba kan talakawa (wato abinda bature ke kira da divide and rule). Idan za’ayi la’akari da kwatanta siyasa irin ta Malam Aminu Kano, wato gwagwarmaya a kan talakawa da sama musu mafita, sai mu ce babu kamar marigayi Abubakar Rimi. Kasancewar Kwankwaso ya sha ruwan wannan bangaren na siyasa, sai ya yi basajen hula shigen ta Aminu Kano da kwaikwayon Rimi. Amma kuma idan mutum ya yi zuzzurfan nazari, sai ya ga cewa siyasar ta kwankwaso dodorido ce ba ainihin irin ta Malam Aminun ba ce.
Daga 1999-2003, Kwankwaso ya yi mulki mai kama da na kama-karya yadda kusan duk manyan ‘yan siyasar Kano sun ja daga da shi, abinda ya kai ga kayar da shi zabe a 2003 duk da ya na kan kujera. Guguwar shari’ar musulunci, shigowar Buhari siyasa da halayen Kwankwaso a shekaru hudunsa sun janyo masa faduwa.
Shekarau da yayi mulki zango biyu a jere, wato daga 2003-2011, shi kuma jirgin guguwar Buhari ya makalewa tare da taimakon malamai ya sami mulkin Kano inda ya yi gwamnatin abokai da malamai da sarakuna. Yadda sai a daf da zai sauka ya waiwaya ya ga babu wani babban aiki na azo-a-gani hatta a cikin kwaryar birnin Kano. Nan da nan ya bada kwangilolin titunan BUK, Ibrahim Taiwo Road da Zoo Road. An yi wadaka da kudin gwamnati wajen bada tallafi iri-iri ga mutane da ke kusa da gwamnati ko wasu a gwamnatin wajen tallafa musu a harkokin asibiti (gida da waje), gina masallatai da makarantu. Ni kaina na sami tallafin da na buga littafina na farko “ASALIN HALITTA DA RAYUWA” a wajen gwamnatin. Sannan anyi kokarin jawo ruwa daga Tamburawa zuwa cikin birni. Alal hakika idan aka yi la’akari da irin kudade da gwamnatin Shekarau ta samu a shekaru takwas muna iya cewa a wajen Talaka, kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Kwankwaso ya samu damar dawowa a Karo na biyu (2011-2015). Ya na shiga gwamnati sai ya baje ayyuka kama da ga ilimi, lafiya, raya kasa da sauransu. A karon farko cikin shekaru gwammai sai ga shi yayan talakawa sun sami damar tafiya karo karatu a kasashen waje, abinda aka daina jin duriyarsa tun lokacin Marigayi Abubakar Rimi a farkon shekarun 1980s. Na yi mamakin yadda Kwankwaso ya yi ayyukan da yayi zuwa 2013, abinda kowa ke tambaya shi ne, ashe gwamnati na da kudin da za ta iya ayyuka haka?. Wannan ya azama ni wajen ganin na tatttara bayanan ayyukansa a wannan lokaci. Na nemi sahalewar Kwankwaso kuma ya bani damar yin aikin mai taken “Manyan ayyukan da gwamnatin Kwankwaso ta aiwatar”. A yayin da na ke wannan aiki na gano cewa Kwankwaso ya gina azuzuwa sabbi guda 800 masu benaye tare da samar da makarantun gaba da sakandare 21. Da farko na yaudaru sosai da wadannan ayyuka amma daga baya na gane cewa ayyuka ne na yaudara domin a wannan lokaci ya na ta hakilon samun takarar shugaban kasa a APC ne. Dadin dadawa, idan ka kalli ayyukan azuzuwa sabbi da aka gina, kusan dukkansu an gina su a bakin hanya yadda za a iya ganinsu, amma wadanda ke sako da lunguna ba a yi musu haka ba. Sannan kuma ginin ne kawai, domin ba a samar da tsarin kujeru da tebura da kayan aiki a cikinsu ba. Har ila yau cikin makarantu 21 da ya samar sabbi, ba su fi guda biyu da suka dore ba zuwa yanzu, amma sauran ko sun zama a yashe ko an maishe su wani abin. Wato karara ka san tsari ne a ka yi babu shirin ya zama dorarre, amma dai ko ba komai ‘yan Kwangila sun ja kaya.
Ganduje ya zo a shekarar 2015-2023 kuma Kano ba ta taɓa shiga uku irin wadannan shekaru ba. An ga abubuwa na ash-sha iri-iri tare da murkushe talakawa. Za ka ji masu kare gwamnatinsa na cewa an yi ayyukan gadojin sama, kwarai an yi, amma kamar yadda Sunusi Lamido ya soki shirin jirgin kasa zuwa Dawanau da cewa me za’a yi safara a layin dogon da zai tallafi harkokin tattalin arzikiñ jihar da wannan jirgin kasa a iya biyan bashin da za’a ci na Dala biliyan daya? (Sukar da ta janyo masa takun-saka da gwamna har ya kai ga tsige shi). Kimar Kano ta fadi sosai a mulkin Ganduje ganin yadda aka yi badakalar dala, da yadda iyalinsa suka tsunduma dumu-dumu a harkar gwamnati, gine-gine babu tsari a makarantu, kasuwanni har da makabartu, da kuma maganar zaben inconclusive.
Kamar yadda wasu ke fada cewa Kwankwaso zai mulki Kano a zango na uku karkashin Abba Kabir, to da alama dai ko ba komai ya dauko hanyar salon mulkin kwankwaso a zangonsa na biyu. Domin a makonnin farko munga yadda ya zo da fushi ya kama rushe-rushe ba kai ba gindi, wanda aka kiyasta ya janyo asarar kimanin Naira biliyan 126. Wannan kuskure ne babba, kuma ko Gwamna ya gane ko bai gane ba, hakika hakan ya janyo masa rasa magoya baya da dama sakamakon wannan abu da ya yi. Sannan a kwanan nan ya farfado da kai dalibai kasar waje yadda har an tura kashin farko. To, wannan ba laifi ba ne, amma kuma kada ya maimaita kuskuren da kwankwaso ya yi. Wato watsi da ginshikin ilimi wanda shi ne ilimin firamare. Duk wadanda za a tura waje karatu, aikin banza ne ga daukacin al’ummar Kano matukar dai ba a gyara ilimin firamare ba.
Dalilin da yasa duk wadannan gwamnoni namu su ka kasa ciyar da Kano gaba bai wuce gwanintarsu wajen yadda za’a kashe kudaden gwamnati yadda su ke so ba yadda jama’a ke bukata ba, wato bukatarsu, ba ta al’umma ba ita ce a gabansu. Maimakon maida hankali wajen ganin sun samar da hanyoyin samun kudaden shiga ta hanyar samar da ayyukan yi a noma da masana’antu da sauransu. Mulki amana ce kuma duk wanda ya yi mulki da zuciya mai kyau sai Allah ya tabbatar da kimarsa a idon mutane tsawon tarihi. Shi yasa har yau ba a sami gwamnoni a Kano irin Audu Bako da Abubakar Rimi ba domin su jama’a su ka sa a gaba kuma su ka yi musu aiki wanda ga shi nan har yanzu ana ganin aikin kuma ana musu addua.
Idan mu ka yi la’akari da yadda a wadannan shekaru 20 jihar Lagos ta kai matsayin da ta ke a yau, abin takaici ne a kwatanta yadda Kanon ta ke a mulkin wadannan shugabanni uku namu. Babban abin kunya shi ne yadda Kaduna ta zo ta buge mu a tara kudaden shiga. A lokacin da Lagos ke iya tara sama da rabin tiriliyan a shekara, mu ko biliyan dari bama iya tarawa, kuma Kaduna ma ta zarce mu. Na yi imani idan muka yi la’akari da albarkatun kasa, noma da jama’ a, hakika wadannan gwamnoni na mu da sun sa jihar a gaba ba siyarsu da bukatarsu kawai ba, hakika ko da bamu kamo Lagos ba, da lallai mu ke bin ta a na biyu. Wallahi matukar ba mu daina makauniyar siyasa yadda yan siyasa zasu ci gaba da yi mana rufa-ido ba, to ban jin zamu ga canji nan kusa. Wajibi idan muna son tursasa akalar siyasarmu ta yi mana aiki, dole sai mun dauki falsafar cewa “Mu daina son dan siyasa, sai dai aikin alherinsa: haka nan mu dai na kin dan siyasa sai dai mugun aikinsa” ta haka kadai zamu waye mu kuma samar da shugabanni masu son mu, ba wadanda mu ke so ba. Allah ya bamu shugabanni da zasu cece mu su gina mana jiha ba kawunansu ba.
Ali Abubakar Sadiq ya rubuto daga Kano – Najeriya