Ya kamata a tsame hannun shugaban ƙasa wajen naɗa shugaban hukumar INEC – Jega

0
397

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira da a yi muhimmiyar gyara ga dokar zabe ta 2022.

Ya ce duk da cewa dokar zaben za a iya cewa ita ce mafi inganci a tarihin Najeriya, amma ba ta cika ba; domin akwai bukatar a kara yin gyare-gyare don kawar da shubuha, da fayyacewa tare da karfafa wasu sassanta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Jega, ya bayyana haka ne yayin jawabi wurin wani taron kwana biyu da Cibiyar Nazarin Majalisun Dokoki da Dimokaradiyya ta shirya na bita ga Sanatoci a Jihar Akwa Ibom.

Gyare-gyaren, in ji shi, ya kamata su kasance har da tilasta aika da sakamako zabe ta intanet daga zabuka masu zuwa na shekarar 2027.

Ya kuma ce bai kamata a ce Shugaban kasa ne zai nada Shugaban Hukumar Zabe da Kwamishinonin Hukumar ba don kaucar da hukumar daga gudanarwa bisa bangaranci.

Ya ce kamata ya yi a sake duba dokar domin tabbatar da cewa an warware duk wasu batutuwan da suka shafi kararrakin zabe tare da yanke hukunci kafin ranar rantsuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here