Zargin kisan kai ya sanya gwamnatin Kaduna rufe makarantar Al-Azhar ta Zariya

0
159

Hukumar Kula Da Ingancin Makarantu ta Jihar Kaduna ta rufe makarantar Al-Azhar da ke Zariya kan zargin kashe wani dalibi da duka.

A ranar Asabar ne aka bayar da rahoton mutuwar wani dalibi dan aji uku a sakandare wanda ya rasu kan zargin duka mai tsanani da wasu malamai suka yi masa har suka cire masa hakora.

Rahotanni sun ce malaman sun zane yaron ne bayan ya daina zuwa makaranta na wasu kwanaki sakamakon an bukaci ya maimaita aji bayan ya fadi jarabawar zuwa aji na gaba.

A wata sanarwa da darakta janar na hukumar ta KSSQAA Dakta Usman Abubakar ya fitar a ranar Lahadi, daraktan ya ce Ma’aikatar Ilimi karkashin wakilcin gwamnatin jihar ta kaddamar da bincike kan lamarin.

Ya bayyana cewa sun kai ziyara zuwa Zariya domin tattara bayanai kan hakikanin abin da ya faru a makaratar Al-Azhar Academy wanda a nan lamarin ya faru da gidan su mamacin domin yin ta’aziyya ga iyalansa da wasu abokan karatunsa.

Haka kuma Abubakar ya bayyana cewa sun kai ziyara hedikwatar ‘yan sanda a Zariya wanda a nan ne shugaban makarantar da mataimakinsa ke tsare.

Haka kuma shugaban hukumar ta KSSQAA ya ce sun kai ziyara makabartar da aka binne yaron.

Ya kuma bayyana cewa makarantar ta Al-Azhar za ta ci gaba da zama a rufe har sai abin da bincike ya nuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here