Duk Almajirin da aka samu yana ‘Bara’ a Maiduguri doka za ta yi aiki akan sa – Gwamnatin Borno

0
298

Yayin da gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce za ta hukunta duk wanda aka kama yana bara bayan sanar da haramcinsa a Maiduguri da wasu kananan hukumomin jihar, wasu masu bukata ta musamman sun ce duk wanda aka ga yana bara ba shi da yadda zai yi ne.

Muhammed Mustapha, shi ne shugaban kungiyar masu lalurar gani, kuma daya daga cikin shugabannin gamayyar kungiyoyin masu bukata ta musamman a jihar Borno, ya shaida wa BBC cewa akwai hanyoyin da ya kamata gwamnati ta bi idan ta na so ta taimaki masu bara su daina.

Ya ce,” Abin da ya bani mamaki shi ne kwanannan aka dauki malaman makaranta dubu hudu ko dubu biyar, amma ba a yi aiki da dokar da tsohon shugaban Najeriya ya sa hannu ba wadda ta ce a dukkan aikin da za a dauka a fadin a kasar, to ya kasance an bawa masu bukata ta musamman kashi biyar cikin 100 na adadin wadanda za a dauka aiki.”

Ya ce,” A cikin nakasassu akwai wadanda suka yi karatu, amma ba a basu gurbi a daukar malaman da aka yi ba, to sai kawai rana tsaka ace wai an hana bara.”

Muhammed Mustapha, ya ce sau da dama ana yanke hukunci ba tare da na tuntubesu ba.

Ya ce, “ Idan akwai wani shiri da gwamnati za ta y iwa nakasassu na moriya ko na jin dadi, ai muma muna ganin baran kamar kaskantar da kai ne, kuma akwai wasu wuraren ma da ‘yan gudun hijira ne ke bar aba nakasassu ba.”

Masu bukata ta musamman din sun mayar wa gwamnatin jihar martani ne bayan ta fitar da sanarwa a kan haramta bara tana mai cewa kaskantar da kai ne.

Farfesa Usman Tar, shi ne kwamishina yada labarai da harkokin cikin gida a jihar, ya shaida wa BBC cewa,” Bara ba al’adar al’umma ba ne kuma ba addininmu ba ne, kuma dama tun tuni gwamnati ta hana baran.”

Ya ce, “Akwai hukumar tsangaya ta musamman, inda da malamai da kuma almajirai za a ba su taimako don su nitsu su yi karatu ba sai sun fita sun yi bara ba.”

Ya ce, daga yanzu tun da an sanar da haramcin bara, to ba a son aga kowa a titi yana bara, idan har aka mutum to doka za ta yi halinta, inji shi.

Ana dai danganta yawan barace-barace a kan tituna a jihar ta Borno da matsalar yan gudun hijira wadanda rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here