Dalilan da ya sa Kotu ta kori shugaban marasa rinjayen majalisar dattawan Najeriya daga kujerarsa

0
265

Kotun daukaka kara a Abuja ta soke zaben shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan Najeriya Sanata Simon Mwadkon, inda ta bukaci sake gudanar da zabe a mazabar sa ba tare da shi ba.

Kotun ta ce matsayin alkalan shi ne Jam’iyyar PDP a Jihar Filato bata bi umurnin kotu na gudanar da zaben shugabanninta a kananan hukumomi 12 kamar yadda ta bada umarni ba, saboda haka jam’iyyar ba ta da hurumin tsayar da ‘dan takara.

Alkalan kotun sun bada umarnin gudanar da sabon zaben wanda zai wakilci mazabar Filato ta Arewa a majalisar dattawa a cikin kwanaki 90 saboda abinda suka kira kin bin umarnin kotu.

Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da kotunan zabe suka soke zabukan da jam’iyyar PDP ta samu nasara na kujerun majalisun tarayya a Jihar Filato, ciki harda na kujerar ‘dan majalisar dattawa da ke wakiltar Filato ta kudu, wadda tuni kotu ta mikawa ministan kwadago Simon Lalong.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here