
Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ya kamata a samar wa mataimakan gwamnoni ayyukan yi a cikin kundin tsarin mulkin kasa, mai makon ‘Zaman ƴan aike ‘ da suke yi a ofisoshin su.
Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a taron shekara-shekara na kungiyar Tsoffin Mataimakan Gwamnonin Najeriya (FFDGN) mai taken: “Hadin kai tare da manufa bai daya don samar da shugabanci na gari da ci gaba mai dorewa” a Abuja.
Ganduje, wanda mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa (Kudu), Emma Eneukwu, ya wakilta, ya bayyana cewa samar wa mataimakan gwamnoni ayyukan yi a kundin tsarin mulki zai kawo ƙarshe matsaloli da rikici da ake samu tsakanin gwamnoni da mataimakansu.
“Na yi farin cikin ganin ku gaba ɗaya da kuka haɗa kanku domin kurkiro da irin wannan kungiya don cigaban ƙasa da ku kanku.
Haka nan shima Sakataren gwamnatin tarayya George Akume, ya hori gwamnoni da su rika keɓance wasu ayyuka na musamman zuwa ofishin mataimakan su.
” Gwamnoni su dai rungume komai sai su, su rike keɓe wasu ayyuka su ba mataimakan su suna yi.
Mataimakan gwamnoni sun zama kamar ‘tayan baya’ kamar yadda wasu ƴan siyasa ke faɗi. Ba su da abin da suke yi sai wakiltar gwamnoni a wuraren sha’ani ko tarukka.