Ɗimuwa da fargaba ta mamaye zuƙatan iyaye da ma sauran ‘yan mata a jihar Neja.
Wannan lamari ya samo asali ne dalilin wani hali da aka tsinci kai na wayar gari da samun labarin wata ɗaliba ‘yar sakandare ta rasa mamanta, daga gaishe da wata Mata.
Budurwar ta na fahimtar hakan nan take ta koma gida a firgice sannan ta sanar da iyayenta halin da ta shiga. Daganan ne suka nufi wajen jami’yan tsaro don bayyana ƙorafinsu.
Sai dai mutanen da ke tare da matar, sun tayar da rikicin ba wanda ya isa ya tafi da matar, kasancewar maman budurwar ya dawo, sai aka haƙura ba tare da sun tafi da ita ba.
Mutane da dama dai na shakkun irin wannan abu da ke ci gaba da faruwa. Sai dai wani mutum da aka tattauna da shi ya bayyana cewar ba wani abu da mutum ba zai gani ba a wannan zamani. Sai dai kawai ana ta addu’a.
Da aka tuntuɓi kakakin ‘yan sandan jihar Neja DSP Abiodun akan lamarin, ya sanar da cewar irin waɗannan labarai ba su da tushe ko gaskiya. Ya kamata mutane su ci gaba da gudanar da rayuwarsu ba tare da wata matsala ko fargaba ba.