Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatis Sunnah ta yi Allah wadai da kira na musamman kan makircin da yahudawa ke yi wa ƙasar Palasɗin.
Kiran ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau yayin gabatar da wa’azin kasa wanda ya gudana a garin Katsina cikin makon da ya gabata.
Shugaban ya buƙaci majalisar ɗinkin duniya ta ɗauki mataki kan zaluncin da yahudawa ke yi wa Palasɗin, a bawa ‘yan Palasɗin haƙƙinsu.
Shugaban ya ƙara da cewa, duk wani ƙuduri da aka kawo na zaman lafiya, yahudawa sai su ta ke. Majalisar dinkin duniya bai zamanto ta bada ma’ana ba idan ya zamanto ba za’a iya ƙwatowa Palasdinawa hakkinsu ba.
Bugu da ƙari ya yi kira ga dukkan al’umma su ci gaba da addu’a, Allah ya yi maganin waɗannan yahudawa azzalumai inda daga ƙarshe ya buƙaci waɗanda ke da hali su taimakesu da dukiya, abinci da magani domin ƙasar yan uwan mu ne musulmai.
Shugaban majalisar malamai na ƙungiyar Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo na daga cikin maluman dake sahun gaba wajen kiranyen tare da neman al’umma su taya ƙasar Palasɗinu da addu’a.