Sharrin sheɗan ne ya haddasa muka samu ƙaruwa da budurwata – Amsar Wani Magidanci a Kotu

0
347

Wani ɗan kasuwa Hamisu Yahaya ya bayyana cewar tsantsar sharri da laifin Sheɗan ne da har ya haddasa suka samu ƙaruwa da budurwarsa.

Malam Hamisu ya bayyanawa kotun da ke Kubwa a Abuja cewar, ya yi nadamar halin da yake ciki. Kuma shi burinsa su samu masalaha da Maryam.

Tun da farko dai Maryam Muhammad ita ta shigar da ƙara akan Hamisu Yahaya kasancewa ya kasa biyan kuɗin makarantar ‘yar su da suka haifa tare da shi.

Ta ƙara bayyana cewar idan har zai iya karɓar yarinyar to ita ba matsalarta ba ce. Kasancewar iyayenta ba su da damuwa akan yarinyar da suka haifa, don su na zaune da juna lafiya.

Sai dai da aka waiwaya ɓangarensa, ya sanar da kotun cewar ko da wasa mahaifiyarsa ba za ta riƙe masa yarinyar ba. Don haka shi dai ya na son su sulhunta komai ba tare da wata matsala.

Daga ƙarshe mai shari’a Ibrahim Rufa’i ya sanar da Maryam cewar a zaman kotun na gaba, da ta zo da yarinyar da kuma sabuwar buƙatarta ga Hamisu Yahaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here