Jami’an tsaro sun daƙile yunƙurin kai harin Boko Haram a Kano

0
427

Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar hukumar tsaro ta farin kaya sun yi nasarar daƙile wani hari na Boko Haram a jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar Birgediya Janar Onyema shi ya sanar da hakan ranar Juma’a 3 ga watan Nuwambar 2023.

Ya bayyana cewar haɗin gwiwar runduna ta uku da kuma hukumar tsaron farin kayan sun yi nasarar kai wani sumame wata maɓoyar masu laifin a ƙaramar hukumar Gezawa da ke jihar Kano.

Mista Onyema ya yi nuni da cewar wannan nasarar aiki da aka samu ita ta hana faruwar yunƙurin kai harin Boko Haram a wani sashi na jihar Kano.

A lokacin samamen, an yi nasarar kame mutane biyu, sai harsashi na bindiga ƙirar AK47, kwanson alburusai, gurneti, da kuma sinadaran kayan haɗa abubuwa masu fashewa sai kuma kayayyakin kaki na jami’yan tsaro, da dai sauransu.

Idan za a iya tunawa a kwanakin nan gwamnonin Yobe da Maiduguri sun fara bayyana damuwarsu yanda wasu tsirarun ‘yan Boko Haram ke son dawo da hannun agogo baya a yankunansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here