Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Kai Fatima Shu’aibu Da Ke Fama Da Cutar Da Ta Kusa Cinye Rabin Fuskarta Asibiti Domin Yi Mata Aiki

0
453

Bayan ganawar da Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Kano ya yi da Fatima Shu’aibu da iyayenta a farkon makon nan a gidansa da ke Kano, ba tare da ɓata lokaci ba ya jagoranci wata tawagar ƙwararrun likitoci zuwa gidan su yarinyar, inda likitocin suka duba ta sannan suka bayar da shawarwarin aikin da ake buƙatar a gaggauta yi mata.

Daga nan ne aka garzaya da ita zuwa wani asibiti a Kano mai suna UMC Zahir, wanda yake da kayan aiki da ƙwarewar magance cutar, inda aka gano tana fama da cutar DAJIN FUSKA, saɓanin cutar da mutane suka riƙa tunanin tana fama da ita a baya kamar yanda me magana da yawunsa Sani Ibrahim Paki ya bayyana.

A cewar Shugaban asibitin, Dr Aminu Garba, yadda za su yi aikin shi ne za su cire ruɓaɓɓen ɓargo daga fuskarta, a yi mata dashen leɓenta na sama da kuma a hancinta, sannan a dasa mata kumatu da leɓen ƙasa da kuma gefen bakinta. Daga ƙarshe kuma za su gyara fuskar tata ta yadda za ta yi kusa da yadda take kafin ta samu cutar.

Idan za a iya tunawa, Hon. Kofa ya yi alƙawarin biyan dukkan kuɗaɗen da ake bukata don nema wa Fatima, mai shekara biyar, lafiya, tare ɗaukar ɗawainiyar da iyayenta za su yi, har sai ta warke gaba ɗaya. A ƙoƙarin cika alƙawarin, yanzu haka likitoci suna kanta, kuma sun ce suna da yaƙinin za ta samu lafiya kuma fuskarta za ta koma kusan kamar yadda take a baya, idan aka kammala bin matakan aikin da za a yi mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here