Jam’iyyar adawa ta NNPP a Najeriya ta nuna aniyarta ta shiga jam’iyyar haɗaka da sauran jam’iyyun adawa kamar yadda Atiku Abubakar ya nema a makon da ya gabata.
Ɗan takarar na jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban Najeriya na 2023, Atiku ya zargi APC da yunƙurin mayar da Najeriya bin tsarin jam’iyya ɗaya sannan ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su dunƙule don yin waje da jam’iyyar mai mulki.
Shugaban riƙo na NNPP na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya faɗa a yau Talata yayin wani taron manema labarai cewa kiran na Atiku abin a yaba ne.
“NNPP na kallon wannan kira na Atiku a matsayin na kishin ƙasa kuma abin maraba,” in ji shi. Sai dai ya ce suna so a yi wa shirin kwaskwarima.
“Sai dai kuma NNPP na son a sauya wa shirin fuska. Muna ganin ya kamata abin ya ƙunshi kowa da kowa, kuma a faɗaɗa shi. Irin wannan haɗakar jam’iyyu suka yi a 2015 wadda ta ba su damar kayar da jam’iyya mai mulki ta PDP a lokacin.
“Saboda haka muna ganin kiran da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubkar ya yi abin yabawa ne.”