Ba haka naso ba! Cewar matashiyar da aka yi wa tiyatar gyaran Hanci.

0
292

Wata matashiyar budurwa ta shiga ruɗani da damuwa bayan da likitoci suka tabbatar mata tiyatar da aka yi wa Hancinta ba za ta kuma sauya yanayi ba.

Bayan ta ƙare nazartar yanda aikin ya kasance ne, sai kawai ta fashe da kuka cikin nadamar halin da za ta shiga.

A cewar Jennifer, wacce ta bayyana labarin a dandalin fesbuk, ƙawarta ta kashe kuɗi mai yawa don yi mata kwaskwarimar gyaran Hanci, wanda suke kira da “Nose Job” a turance.

Mutane da dama ne dai ke biyan kuɗi don a yi wa wasu sassan jikinsu kwaskwarimar da za ta sa su birge al’umma, wanda hakan ya fi yawa ga Mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here